Talata 23 Yuni 2026 - 14:20
Ta Yaya Makarantar Tunanin Imam Ruhullah (Q) Da Shahidin Jagora (Q) Suka Sauya Ma'aunin Iko? "Ba Ma Yin Zalunci Kuma Ba Ma Karɓar Zalunci"; Babbar Ka'idar Jagoranci A Gwamnatin Juyin Juya Hali (3)

Hauza/ Wannan kashi na uku ne na fassarar tattaunawar da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza yayi da Hujjatul Islam Mumini, masani kuma mai bincike a kan Juyin juya halin Musulunci.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Lokacin da Imam Khumaini (Q) Ya Yi Magana Akan Shafe Kasar Isra'ila

Imam Khumaini (R) ya fuskanci sarki (Shah) kai-tsaye ta hanyar jawabi, sannan ya bayyana cewa Musulunci yana cikin hatsari inda ya nunawa malamai da mutane, kuma ya yi magana akan Isra'ila inda ya fayyace cewa dole ne a kakkabe Isra'ila kuma a shafe ta baki daya. Wato kalaman da a yau muke amfani da su cikin sauki a gaban haramtacciyar daular sahyoniyawa kuma muke tsayuwa a bayyane a gabanta, a wancan lokacin ma sun fito ne daga bakin Imam cikin daukaka da karsashi.

Wancan lokacin, shekarar 1963 ko 1964 Miladi ce; lokacin da Isra'ila take kololuwar ikonta, inda ta fafata yaki da dakarun kasashen Larabawa ta kuma yi nasara a kansu baki daya. Wancan lokacin ba kamar shekarar 1404 ko 1405 (Kalandar Shamsi / daidai da 2025-2026 Miladi) ba ne da Isra'ila ta wulakanta ta kuma kaskanta har zuwa wannan mataki; duk da haka, Imam Khumaini ya bayyana maganarsa cikin karfi da fito-na-fito. Saboda haka, idan muka sanya wadannan abubuwa a gaba, za mu iya fitar da dabarun yunkurin Imam.

A gaskiya Imam Khumaini ya aiwatar da wasu muhimman ayyuka waɗanda a yau za mu iya kiransu da "Misali" ko "Tsari". Shugabanmu Shahidi (Ayatullah Khamenei) shi ma ya bayyana wadannan abubuwa a cikin wasu sassa na bayanansa. Ni a nan zan lissafa su dalla-dalla daki-daki sannan in kawo takaitaccen bayani a kansu.

Daya daga cikin wadannan abubuwa shi ne cewa Imam Khumaini ya rushe dukkan tsarin raba kan mutane gida biyu. Kamar yadda kuka sani, daya daga cikin ayyukan da 'yan siyasar duniya suke yi, kuma har yanzu suke ci gaba da yi domin jefa al'ummomi cikin rudani, shi ne cewa a koda yaushe suna sanya su a tsakar rarrabuwar hanya guda biyu.

Wannan abu ya faru a lokacin fafutukar gudanar da mulki na doka (Mashruteh) ma. Misali, sun ce mutane ko dai masu son Mashruteh ne ko kuma masu goyon bayan mulkin kama-karya; wato kamar babu wata hanya ta uku. Sun gina yanayin ta yadda idan wani ya ce ni ba mai mulkin kama-karya ba ne kuma ban amince da wannan Mashruteh ba, ina da wani ra'ayi na daban, kamar yadda Sheikh Fazlullah ya fada inda ya kawo batun "Mashruteh Mashru'eh" (Mataimakin doka na addini), nan take sai su lakaba masa sunan mai mulkin kama-karya kuma su bayyana shi a matsayin mutum mai zalunci har zuwa lokacin da suka kai ga yi masa kisan gilla (shahada).

Hadakar Addini da Siyasa; Kore Tsarin Secularism a Aikace

Imam Khumaini (R) ya rushe wadannan tsare-tsare na rarraba kai. Imam ya sanya addini da koyarwar gaskiya tare da siyasa kafada da kafada; aikin da babu wanda ya taba yin irinsa har zuwa wancan lokacin. Wannan al'amari yana nufin kore tsarin Secularism (raba addini da siyasa) kai-tsaye a aikace. Kuma abin sha'awa ne mu sani cewa ainihin tsarin Secularism a wancan lokacin yana daya daga cikin manyan shika-shikan siyasar zamani na duniya a karni na ashirin.

A wancan lokacin, gudanar da siyasa yana daidai da kasancewa mabiya Secularism; wato duk lokacin da kake son nuna kanka a matsayin dan siyasa, dole ne ka rika cewa ba ka da wata alaka da addini. Ainihin fassarar siyasa ba ta da wani hoto na daban da ya wuce wannan.

Tabbas a wani lokaci, Shahid Mudarris ya kasance yana cewa: "Siyasarmu ita ce addininmu, kuma addininmu shi ne siyasarmu", kuma malamanmu sun bayyana wannan ma'ana; amma a kololuwar tsarin kasancewar daula guda daya mai iko a duniya karkashin jagorancin Amurka, an fassara siyasa a matsayin tsarin Secularism wanda ya yanke kansa daga addini, koyarwa na gari, da dukkan abin da yake da kamshin dabi'u da al'adu.

Kokarin Ijtihadi Mai Karfi; Hadaka Tsakanin Dokokin Musulunci da Bukatun Zamani

Wani muhimman abu kuma shi ne cewa Imam Khomeini (R) ya bayyana cewa dole ne mu aiwatar da dokokin Musulunci; aiwatar da dokoki, tare da la'akari da maslaha da bukatun zamani, abubuwa ne da za su iya tafiya tare.

Ba wai mu ce domin muna son mu yi la'akari da bukatun zamani ba, sai mu ce dokokin Musulunci na gargajiya ne saboda haka ba za su iya aiki ba; Imam ya ce sam ba haka ba ne. A gaskiya, idan kuka lura da kyau, wancan Ijtihadi mai karfi da inganci na zamani wanda Imam yake nufi, ana iya fitar da shi ne daidai daga wadannan tushe.

Abu na gaba shi ne cewa Imam Khumaini (Q) ya jaddada kafa adalci tare da samar da dukiya da arziki na kasa. Ya bayyana cewa mu muna adawa da tsarin jari-hujja (Capitalism); ba ma son dukiya da arziki su takaita a hannun wasu gungun mutane kalilan na musamman. A lokaci guda kuma, muna amincewa da samar da dukiya kuma dole ne kasa ta samar da arzikinta ta kuma tsaya akan kafafun da kanta, amma wannan abu ba shi da wata adawa da tabbatar da adalci. Kuna iya samar da arzikin kasa kuma a lokaci guda ku kafa adalci na gari. Wannan shi ma yana daya daga cikin sauran tsare-tsaren da muke gani a cikin tunanin makarantar Imam.

Babban Tushe: Ba Ma Yin Zalunci, Kuma Ba Ma Karbar Zalunci

Abu na gaba shi ne batun kore zalunci da kore mika wuya ga zalunci (Inzilam); wato Imam Khumaini (R) ya ce mu ba ma yin karfi na zalunci kuma ba ma taba mika wuya a karkashin karfi na zalunci. Maganarmu a fili take. Muna da hujjoji masu karfi kuma muna da hankali na kwarai a fagen shugabanci.

A daidai nan, ya kamata mu bayyana wannan batu cewa, wata babban siffa mai matuƙar muhimmanci kuma a mahangata yana da kyau a ambata a nan, shi ne cewa shugabancinmu ya yi daidai da hankali da tunaninmu na kwarai; wato ba ma fadin wata magana da ta fita daga tsari. Wadanda suke fadin magana ba tare da tsari ba su ne Amurkawa.

Sabanin Kasashen Yamma akan Batun Nukiliya

Misali, game da batun makamashin nukiliya, ku duba irin sabanin da Amurkawa ke da shi. Makamashin nukiliya na zaman lafiya wani abu ne da muka kwashe shekaru sama da ashirin, wato kusan shekaru ashirin da hudu ko ashirin da biyar muna gwagwarmaya a kansa; domin wannan damar ta kasance a matsayin arzikin kasa a hannunmu kuma ta rage domin tsararraki masu zuwa. Amma Amurka tana hana mu wannan hakki namu.

A gefe guda kuma, su da kansu ba wai kawai suna amfani da makamashin nukiliya ba ne, a'a har ma sun kera bam din atom (Atomic Bomb) kuma su kadai ne kasar da ta taba amfani da shi a tarihin duniya. Saboda haka Imam Khumaini (Q) yana cewa mu ba ma mika wuya a karkashin zalunci, ba ma yin zalunci, kuma ba ma mika wuya a gaban maganar zalunci sam.

Rarraba Kai akan Batun Tsaro da Ci Gaba

Abu na gaba shi ne cewa Imam Khumaini ya bayyana cewa dole ne mu karfafa kasar ta fuskar kimiyya da tattalin arziki, sannan a lokaci guda mu karfafa garkuwar tsaron kasa. Wannan al'amari a wadannan ranaku ya fito fili sosai kuma ana jin sa a aikace; domin wasu mutane a nan ma sun samar da rarrabuwar kai. A cikin wadannan shekaru goma ko sha biyar na baya-bayan nan, ana cewa wadannan abubuwa guda biyu ba za su iya haduwa wuri guda ba; suna cewa idan har wata kasa ta yi karfi ta fuskar tattalin arziki, hakan ya faru ne saboda ta aje garkuwar tsaronta na kariya a gefe, kuma suna kawo misalai da kasashen Japan da Jamus domin tabbatar da wannan da'awa tasu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha